Hasalallun Direbobin Keke Napep a Abuja sun babbake ofishin VIO dake unguwar Idu dake Abuja.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne matuka Keke Napep suka rufe hanyoyi a Unguwannin Utako dake Abuja a zanga-zangar nuna fishin su ga jami’an VIO.
Da yawa cikin su sun koka kan yadda VIO ke muzguna musu sannan da yadda suke musu kwace karfi da yaji a Abuja din.
A wannan rana sun farfasa Kekuna aama da 50 sannan.
A maida martani da ake zargin direbobin Keke Napep dinne suka aikata sun, a daren juma’a suka garzaya ofishin VIO din dake Idu suka banka mata wuta.
Jami’in VIO da ya zazzagaya da wakilin PREMIUM TIMES, babbakakken ofishin ya ce suna zargin direbobin Keke Napep dinne suka aikata wannan aiki.
” Kamar yadda muka sami rahoto, sun far wa ofishin ne cikin dare inda suka banka mata wuta.
” Babu abin da suka bari domin komai ya kone kurmus.
Ko da yake ba a tabbatar cewa ko direbobin Napep din ne suka aikata haka, an dade ana kai ruwa rana tsakanin VIO da masu tuka baburan Keke Napep din a Abuja.
Discussion about this post