Jijjigar kasar Abuja fa ba abin wasa ba ce – Daraktan Gine-gine

0

Darakta Janar Danladi Matawal na Cibiyar Binciken Gine-gine da Titina, ya yi gargadin cewa kada fa Najeriya ta yi wa afkuwar jijjigar kasar da ta faru a Abuja rikon-sakainar-kashi.

Cikin wani bayani da ya fitar, ya ce tabbas akwai bukatar gwamnati ta gaggauta binciken musabbabin faruwar wannan jijjigar kasa a Babban Birnin Tarayya, Abuja, wadda ta afku a sassan Abuja a ranakun Alhamis da Juma’a.

Ya ce akwai bukatar Najeriya ta fito da tsarin da zai magance sake faruwar wannan jijjigar kasa, ya-Allah ko dalilin hakar kasa ne ta faru ko kuma a’a.

“In dai akwai inda aka rarake karkashin kasa ana gina titin karkashin kasa ko yin wani gini a karkashin kasa, to wannan gini kan iya kumbura jijiyoyin kasa har su fara jijjiga.” Inji Matawal.

“Su kan su mazauna Abuja na matukar bukatar da a horas da su matakan gaggawar da ya kamata su dauka a cikin hanzari, idan irin haka ta sake kasancewa.

“ Idan wannan jijjiga kaddara ce daga Allah Ta’ala, to fa sai a yi shirin fara kwashe mutane daga Abuja ana ficewa, domin ita babbar girgizar kasa fa ta kan fara ne da ‘yar jijjigar kasa, dalili, saboda karkatsewa da daddatsewar da igiyoyi ko jijiyoyin karkashin kasa ke yi ko kuma saiwa-saiwar da ke rike da farantin da ke tallabe da jijiyoyin karkashin kasar su kan su.” Gargadin Matawal kenan.

“ Wato aman wutar duwatsu da girgizar kasa duk wani balbalin bala’i ne wadanda Najeriya ba ta ma taba tunanin yi musu shirin ko-ta-kwana ba. To saboda ba a taba shirya musu din nan ba, sai jikin mu ke ba mu cewa kamar ba mu ma san da su ba, ko kuma ba mu yarda za su iya faruwa a nan ba.”

“ Zan ja hankalin mu da cewa wani ya ba mu labari cewa a inda ya ke a garin Mpape, inda jijjigar kasar ta fi karfi, kare ya fara ji ya na ta haushi ba kakkautawa. Jin haka sai mu ka yi ta rafka addu’a cewa Allah dai ya sa wannan abu ba wani ibtila’i ba ne daga Allah.

“ Domin idan ibtila’in girgizar kasa ce, to gargadin farko da jama’a za su fara ji shi ne dabbobi su fara firgita su na haushi, su na fafarniya.

“Za a ga karnuka sun kaure da haushi ba kakkautawa, maguna su kasa zaune, su kasa tsaye wuri daya, su na ta sagarabtu, beraye su rika gig-gilmawa cikin gida ko cikin dakuna a guje, kuma a rude. Dawaki kuma su rika harbin iska da haniniya su na fizge-fizgen tsinkewa daga turakun su, su na fagamniya a rude.”

“Ba wani abu ba ne zai sa su rika yin wannan sai saboda maganadison ji da sauraren su ya sinsino kuma ya fizgo musu karkarwar da karkashin kasa ke fara yi a lokacin da jijiyoyin karkashin kasa ke daddatsewa daga jikin farantin da ke tallabe da karkashin kasar baki daya.”

Ya ce mataki mafi sauki da kuma saurin dauka idan irin haka ta faru, to a yi gaggawar ficewa daga inda ake, a kwashi yara da kananan dabbobin da za a iya runguma, a runtuma a guje zuwa cikin fili ko sararin da babu gine-gine kusa.

Matawal ya ci gaba da bayar da wasu misalai da alamomin matakai har guda hudu masu nuni da cewa idan hakan ta auku, ko kuma ta fara aukuwa, to babu makawa girgizar kasa na tafe.

Share.

game da Author