Gwamnan jihar Adamawa Muhammadu Bindow ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta maida hankali wajen samar da ababen more rayuwa ne ga mutanen jihar a shekara mai zuwa.
Bindow ya fadi haka ne da yake sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2018 da aka yi a fadar gwamnati dake Yola.
Bindow ya yabi majalisar dokokin jihar na kammala nazari a kan kasafin kudin 218 cikin lokaci.
” Ina tabbatar muku da cewa wannan itace karo na farko da majalisar dokoki a jihar ta kammala nazari kan kasafin kudi cikin dan kankanin lokaci.”
Ya kuma Kara da cewa gwamnati za ta wadata ‘yan majalisar 25 da kudi naira miliyan 500 domain hi wa mutanen da suke wakilta ayyuka na musamman.
Daga karshe Bindow ya yabi ma’aikatan jihar game da irin goyan bayan da suke ba Wannan gwamnati.
” Ina mai tabbatar muku da cewa gwamantin mu ta kammala biyan bashin albashin ma’aikata na watanni 7 wanda ta gada daga gwamnatin da suka baya.”