SAKACIN EFCC: Kotu ta bude wa Patience Jonathan Asusun Ajiya 16 a bankuna

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta janye umarnin da ta bayar na a rufe dukkanin asusun ajiyar uwargidan tsohon shugaban kasa, Patience Jothanan, har guda 16, saboda EFCC ta kasa gudanar da bincike a cikin kwanaki 90 da kotun ta ce a yi binciken.

Babbar Mai Shari’a Binta Murtala Nyako, ta bada umarnin a bude wa Patience dukkan asusun ajiyar na ta, sakamakon rokon da lauyan Patience ya yi, tunda EFCC ta kasa gudanar da binciken da aka ce ta gudanar a cikain kwanaki 90.

Lauyan ta mai suna Mike Ozekhome, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kotu ta umarci EFCC da ta binciki asusun guda 16 na Patience, amma ta kasa aiwatar da haka.

Dama dai EFCC din ce ta garzaya kotu ta kai karar cewa kudaden da ke cikin asusun 16 na uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, akwai harkalla da wuru-wuru a hanyoyin da aka tara kudaden.

An yi ta sa-toka-katsi a kotu, inda daga karshe kotu ta ce a rufe dukkan asusun, amma ita EFCC ta je ta yi bincike a cikin kwanaki 90, ta kai wa kotu hujjujin cewa kudaden na harkalla.

Kasa gudanar da binciken da EFCC ta yi ne kotu ta bayar da umarnin cewa a sakar wa Patience Jonathan dukkanin asusun na ta 16 da aka rufe.

Share.

game da Author