Wani Magidanci ya sha da kyar a hannun matarsa

0

Wani magidanci Taoheed Hassan ya roki kotu ta warware aurensa da matarsa Blessing.

Ya ce ba zai iya ci gaba da zama da matar tasa ba don tana so taga bayan sa.

Taoheed Hassan ya bayyana cewa blessing ta nemi ta raba shi da ransa ne don ya tsawata mata akan yawan yawace-yawacen da ta ke yi a matsayinta na matan aure sannan da rashin kula da ya’yansu uku.

Ya ce a duk lokacin da yace zai rabu da ita sai ta ce zata zuba masa guba a cikin abinci ko kuma ta caka masa wuka.

Da take amsa laifinta Blessing ta yarda a warware auren.

Ta fada wa kotun cewa ta nemi ta kashe mijinta ne domin shi ya fara neman ya dauke nata ran.

Bayan da ya gama sauraren su alkalin kotun Ademola Odunade ya yanke hukuncin raba auren.

Alkalin ya ce manyan ya’yansu biyu za su zauna da mahaifinsu Taoheed shi kuma karamin zai zauna da mahaifiyarsa Blessing.

Share.

game da Author