Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo sun yi nasarar cafke wasu matsafan da su ka kashe wasu dalibai uku, kuma su ka yanke nonuwan su, su ka sayar a kan naira milyan 12.
Wadanda aka kama din dai sun kuma bayyana cewa su ne su ka sace dalibai mata a kwalejin ilmi ta Adeyemi da ke garin Ondo.
Da ake faretin nuna su ga manema labarai a Akure ranar Alhamis, sabon Kwamishinan ‘Yan sanda. Gbenga Adeyanju, ya ce wadanda ake zargin sun sha aikata manyan laifuka, har ma ta kai su na tsallakawa makwautan jihohi, su tabka ta’asa su gudo.
Ya ce wadanda ake zargin dai, John Adenitire, Fisayo Fasanu, Abdurafi’u Tijjani an kama su ne a wurare daban-daban, kuma sun fada da kan su cewa su ne su ka kashe daliban kwalejin ilmi ta Adeyemi da ke Ondo.
Ya ce tun a ranar 28 Ga Yuli aka kai wa ‘yan sanda rahoton bacewar daliban. Sannan ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin, wato Adenitire, an kama shi ne yayin da aka ritsa da shi a wurin wani fashi da makami a Ondo, inda shi ma ya bada labarin ya na daya daga cikin masu sata da kame yara su na sayar wa matsafa, ciki kuwa har da daliban nan uku.
‘Yan sanda sun ce Adenitire da Fasanu sun furta cewa sun sayar da sassan jikin daliban ne ga wani mutum mai suna Tijani a garin Ore, wanda ya yi musu alkawarin biyan su naira milyan 15.
Amma kuma Adenitire ya ce har yau wannan matsafin bai ba su ko sisi ba,
“Sun yi alkawarin biyan mu naira miliyan 5 a matsayin fasashin kudin nonon bangaren hagu da kuma hannun hagu. Sai mu ka aika musu da gawarwakin ‘yan mata uku. Amma ba su kai ga biyan mu kudin ba, sai ‘yan sanda su ka kama mu.”
“Bayan mun kashe ‘yan matan uku, mun kuma cire nonuwan su, sai muka rufe gangar jikin su a cikin jeji, mu ka bai wa Alfa da Sile wanda ya na cikin guruf din mu, amma shi ya tsere yayin da ‘yan sanda suka cim mana.”
“Ba da ni aka yi kisan ba, amma dai na san na tsaya daidai hanyar shiga cikin jejin ina sa-ido don kada wani ya zo ya ga abin da ake aikatawa.”