An Kama ministan Buhari da yin zambar miliyan 12 kudin gwamnati

7

A wasu bayanai da ofishin Odita Janar na kasa ya fitar kan wasu bincike da suka gudanar a ma’aikatan ayyukan mata, ya nuna cewa ministan mata Aisha Alhassan ta karbi wasu kudade daga ma’aikatar domin yin ziyarar wasu wuraren ayyukan gwamnati da ma’aikatar ta ke kula da su da ba haka bane.

Binciken da aka gudanar sun nuna cewa karya ne ta shirga wajen karbar wadannan kudade domin duk bayanan yadda aka kashe kudaden bai saje da takardun da ta mika ba.

Bayan haka ana gano cewa wadannan ayyuka da tace za ata je dubawa basu.

Yanzu dai an umurci Aisha Alhassan da ta maida wadannan kudade asusun gwamnati.

Share.

game da Author