Kungiyar Kwallon kafa ta Bayern Munich da ke kasar Jamus ta ladabtar da takwaranta ta Arsenal da ci 5 da daya a wasan kwallon kafa na zakarun nahiyar turai da aka buga yau.
Yadda kasan uwa da danta ta inda Bayern ke shiga ba tanan take fita ba.
Arsenal ta samu zura kwallo daya ne ta hannun dan wasan ta Alexis Sanchez.
Rueben, Lewandoski, Thiago da Thomas Muller ne suka zura kwallayen a ragar Arsenal.
A wasa ta biyu kuma, Real Madrid ta doke Napoli da ci 3 da 1.