Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta hada kawance da jihar Kaduna

1

Mataimakiyar gidauniyar Bill and Melinda Gates, Melinda Gates ta yaba wa gwamnar jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I akan kokarin da yake yi a jihar na ganin cewa an samu raguwar mutuwar yara kanana musamman ‘yan kasa da shekara 5.

Melinda Gates ta kuma ce gidauniyar a shirye take ta taimakawa jihar musamman yadda gwamnatin jihar take nuna kwazo wajen aiwatar da ayukkanta ayyukan da ya shafi kiwon lafiyar mutanen jihar musamman kanana yara.

Ta kuma ce sakamakon aikin rigakafin da jihar ta nuna mata ya gamsar da ita kuma tana so ta hada kawance da jihar kaduna domin gidauniyarta ta taimaka ma cibiyoyin kiwon lafiyar jihar domin samar da ingantacciyar kiwon lafiya ga mutane yadda ya kamata.

Gwamnar jihar Nasir El-Rufa’I ya nuna godiyarsa mutaka akan taimakon da jihar Kaduna za ta samu akan hakan.

Share.

game da Author