Babu ruwan mu a rikicin yankin Kudancin Kaduna – Inji Kungiyar Miyatti Allah

0

Kungiyar makiyaya Fulani ‘Miyatti Allah’ ta musanta zargin da akeyi mata cewa wai da hanunta a cikin rikicin yakin kudancin Kaduna.

Mataimakin shugaban kungiyar Ibrahim Abdullahi ya ce sun musanta zargin ne saboda labaran da ake wallafa a jaridar Vanguard dauke da sunan wani dan jarida mai suna Luka Binniyat da ya rubuta cewa shugaban kungiyar Miyatti Allah ya tabatar da hanun kungiyar a rikicin yankin kudancin Kaduna.

Malam Ibrahim ya yi bayanin cewa zargin duk karya ce kuma suna kalubalantar dan jaridar Luka da ya zo ya bada shaidunsa akan wannan zargin idan ya tabbatar cewa ya na da gaskiya akan irin wadannan korafe korafe da ya yi idan kuma bashi da wadannan shaidu kungiyar Miyatti Allah din na bukatan shi da ya rubuto musus takardar neman gafara akan kazafin da yayi musu ko kuma su kama shi gaban kuliya.

Ya roki jami’an tsaron jihar Kaduna da su binciki zargin domin hukunta masu bata ma Fulani suna.

Ya kuma shawarci makiyayan kasar gaba da kada su biye ma jita-jita musamman akan rikicin kudancin jihar Kaduna kuma su zamanto masu bin doka.

Daga karshe ya roki gwamnatin tarayya da na jihar Kaduna da su yi kokarin ganin dawwamammen zaman lafiya ya tabbata a yankin.

Share.

game da Author