Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yayi kira ga jami’an tsaron kasa da su yi taka tsantsan da yadda suk far ma gidajen jaridu babu gaira babu dalili musamman a wannan lokaci da muka kokarin jaddada mulkin demokradiyya a kasa Najeriya.
Sanata Shehu Sani yayi tir da samamen da aka kai gidan Jaridar PREMIUM TIMES in da yace hakan bai dace ba musamman ganin cewa muna mulkin demokradiyya ne a kasa Najeriya.
Ya ce irin hakan zai iya sa kasashen duniya su dawo daga rakiyar kasa Najeriya musamman ganin cewa aikin jarida na da cikakkiyar ‘yancin ba tare da an muzguna mata ba.
Bayan haka kuma kungiyar kare hakkin dan Adam na Amnesty International sun nuna bacin ransu akan abinda ya faru da gidan jaridar sannan sunce zasuyi bincike akan abinda ya faru domin sanar wa duniya matsayarsu akan abin da ya faru da kamfanin.