Shugaban kungiyar likitocin Najeriya Mike Ogirima ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dawo da hukumar kula da ayyukan likitoci na Najeriya.
Ogirma yace wannan hukuma itace za ta iya tsamo wa da hukunta duk wani baragurbin likita da yake aiki a kasa Najeriya.
Yace hukumar za ta iya koran duk wani likita da ba kwararrebane sannan ta hukuntashi idan ya karya dokar aikin kuma sune suke da ikon ba da lasisi ga duk wani likita da yake aikin kula da lafiyar mutane a kasa Najeriya.
Yace rashin wannan hukuma ya sa wadansu baragurbin likitoci suna ta kashe mutane ba tare da an sa musu tara ba da sunan aikin likitanci a asibitoci dabam dabam a kasar nan.
Bayan haka ya kara da cewa matsalar tabarbarewan tattalin arziki da ya kasa Najeriya ta ke fama dashi yana daga cikin abubuwan da yake hana mutane iya zuwa asibitocin da kararru ke aiki a ciki da kuma iya siyan ingantattun magunguna idan basu da lafiya.
Bayan haka kungiyar a yanzu ta kafa wata kwamiti domin sa ido da kula da irin wadannan likitoci domin kawo karshen irin wadannan ayyuka na likitocin da basu kware a aikin ba.
Daga karshe Ogirima ya roke gwamnati da ta duba kukansu ta dawo da wannan hukuma.