Mun koyo dabarun warkar da cutar tabuwar hankali a kasar Burundi da Rwanda – Likita Wakama

0

Wani babban likitan kwakwalwa Ibrahim Wakama ya sanar da dabarun da suka koyo a kasashen Burundi da Rwanda domin yadda za’a shawo kan matsalar tabuwan hankali da dayawan mutanen arewa maso gabas ke fama da shi saboda ayyukan Boko Haram.

Likitan ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da gidan jaridar Premium Times a taron da kungiyar ‘Development Research and Projects Center DRPC ta gudanar a Abuja.’

Ya yi bayanin cewa abin da likitocin suka tanada domin shawo kan wannan matsalar sun had a da ma’aikata, dabarun yadda za’a shawo kan matsalar da kuma kudaden da suke bukata domin hakan.

Bayan haka kuma ya bayyana cewa sun
koyo dabaru da dama wanda kasashen Burundi da Rwanda suka yi amfanin da shi lokacin da suma suka shiga irin wannan hargitsin a kasashen su.

Ya ce an turo marasa lafiya asibitin su dasu ka kai 1654 sannan kashi 65 daga cikin su mata ne kuma har yanzu da mutane da dama wadanda suke fama da matsalar da ba’a San inda suke ba.

Likita Wakama ya ce matsalolin da suke fama da su shine na karancin kudaden da suke bukata domin siyo kayayyakin aiki, sannan gwamnati har yanzu bata bada nata gudunmawar ba, kuna wasu kungiyoyin da suka saba taimaka musu sun fara janye taimakon na su saboda rashin kudi.

Wasu kwararu likitocin kwakwalwa kamar su Mustapha Gudaji, Faltama Shettima da suka halarci taron sunyi kira ga gwamnati da dasu taimaka domin ganin an samo mafita akan wannan matsala.

Share.

game da Author