A karo na biyu, Bam ya sake tashi kusa da jami’ar Maiduguri

0

Wani dan kunar bakin wake ya ta da bam wani masalacin da ke Dalori kusa da jami’ar Maiduguri da safiyar Talata din nan.

Garin Dalori na kusa da jami’ar Maiduguri ne a jihar Barno.

Tashin bam din ya farune wata cif daya da wani dan kuman bakin waken ya tada wata bam din a cikin masalacin dake jami’ar Maduguri.

Bincike ya nuna cewa dan kunan bakin waken wanda ba zai wuce dan shekara 8 zuwa 10 ba ya tada bam dinne a lokacin da ya gagara shiga cikin masalacin saboda zaman jami’an tsaro a bakin masallacin.

Bam din ta kashe mutum daya ne kawai.

Bayan haka gidan jaridar Premium Times ta nemi Karin bayani daga bakin kakakin hukumar dake bada agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Barno Abdulkadir Ibrahim yace ba za su iya tantance jikin ko na namiji ba ne ko mace ce domin yadda jikin ta yagalgale.

Share.

game da Author