Dan wasan finafinan Hausa kuma mawaki, Adam Zango zai yi wasa a kasar Canada bayan wata gaiyata ta musamman da kasar ta yi masa.
Adam zaiyi wasanne a bukin cikan kasar shekara 150 da kafuwa.
Masu shirya bukin sun ce sun gaiyaci Zango ne domin zama gwani a harkar wasanni da nishadantarwa.
Za ayi bukinne a watan Yulin wannan shekaran.