Adama Barrow zai cigaba da zama a kasar Senegal har sai an rantsar da shi

1

Zababben shugaban kasar Gambiya Adama Barrow zai cigaba da zama a kasar Senegal sai bayan an rantsar dashi.

Za’a rantsar da sabon shugaban kasar Gambiyan ne a ranar 19 ga wannan watan, wato Janairu.

Yahaya Jammeh, wanda ya sha kayi a zaben bayan ya amince da nasarar da Adama Barrow ya samu a zaben yayi watsi da amincewar da yayi daga baya inda yace sam ba sauka ba cewa bai amincewa da sakamakon zaben ba kuma.

Kungiyar ECOWAS ta gana da bangarorin biyu domin kawo karshen takaddamar amma abin yaci tura.

Yahaya Jammeh ya tsaya akan bakan sa na ba zai sauka daga kujeran shugabancin kasar ba.

Share.

game da Author