Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Faisal Shuaib a matsayin babban sakataran hukumar NPHCDA.
Faisal wani babban likita ne kuma ma’aikacin gidauniyar Melinda da Bill Gates (BMGF) da ke kasar Amurka.
Ya kuma yi aiki da cibiyar da take bada agajin gaggawa a shekarar 2014 a matsayin wanda ke kula da kawar da cutar Ebola da kuma wayar da kan mutane akan cutar.
Faisal Shuaib a shekarun 2012 zuwa 2015 ya yi aiki da mai’aikatar kiwon lafiya da NPHCDA a matsayin mai ba da shawara akan rigakafi da kuma kawar da cutar shan inna. Ya kuma yi aiki da babbar jamiyar Alabama da ke kasar Amurka.