Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru ya bayyana cewa nan bada dadewa ba Allah zai tona asairin tsohon mataimakin gwamnan Jigawa Ahmed Mahmoud da ya koma jam’iyyar PDP.
Badaru ya ce ” Shifa Mahmoud bashi tsoron Allah, domin sai ya rantse da Alkur’ani mai girma akan karya kuma ya sani. Shi ko wani irin shirgegen makaryaci ne haka da baya tsoron Allah idan zai kantara karya?
A lokacin da Mahmoud canja sheka daga APC zuwa PDP, ya yi kurin cewa dubban magoya bayan sa yan asalin yankin Gumel duk sun bishi zuwa jam’iyyar PDP, sai dai kuma gwamna Badaru ya karyata wannan furuci na Mahmoud.
Badaru ya ce dukka mutanen Gumel na nan a inda suke wato jam’iyyar APC.
A ci gaba da jawabi da yayi a bainar dubban magoya bayan ‘yan APC a taron jam’iyyar a Karamar hukumar Sule Tankarkar badaru ya kara da cewa duk inda tsohon mataimakin jihar ya samu damar yin jawabi a kowani taro ne sai ya sharara karya, amma kuma ya ce Allah zai tona masa asiri nan bada dadewa ba.
Mahmoud yayi mataimakin gwamna a zamanin gwamna Sule Lamido, daga 2007 – 2015.
Discussion about this post