Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu ya fara fagamniyar da cewa daga PDP, bayan ya yi sanarwar janyewa daga takarar gwamna a zaɓen fidda-gwanin da aka shirya yi na ‘yan takarar gwamnonin PDP a yau Laraba, 25 Ga Mayu.
Kakakin Yaɗa Labaran Tawagar Kamfen ɗin Ike Ekweremadu, mai suna Charles Asuga ne ya fitar da sanarwar janyewa daga takarar fidda-gwani da Ekweremadu ya yi daga ‘yan takarar gwamnan PDP na a Enugu.
Duk da cewa ba a bayar da sanarwar dalilin janyewar sa ba, amma dai tabbas lamarin ba ya rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin sa da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, wanda ke kammala wa’adin sa na shekara takwas cikin 2023.
Haka kuma Ekweremadu na da saɓani da shugabannin PDP na jihar Enugu.
Yayin da Gwamna Ugwuanyi ya nace ya ce sai an bi tsarin karɓa-karɓa wajen tsayar da ɗan takarar gwamna, kamar yadda aka taɓa cimma yarjejeniya a baya.
Shi kuma Ekweremadu ya ce ƙarya ce, babu wata yarjejeniya da aka taɓa cimma a baya ta bin tsarin karɓa-karɓa.
Kwanan baya an yi zaɓen wakilan ‘yan takara na PDP a jihar Enugu, inda aka zaɓi wakilai 260, wato kowace mazaɓa wakili uku, amma babu magoya bayan Ekweremadu ko ɗaya a cikin su.
A ranar Laraba an ga Ekweremadu ya je Hedikwatar APC ta Abuja, inda ake zaton ƙoƙari ya ke yi domin ya samu shiga a cikin jam’iyyar, har ya fito takarar zaɓen fidda gwani.
Tuni dai Gwamna Ugwuanyi ya halifantar da Peter Mbah matsayin ɗan takarar PDP na Gwamnan Enugu.
A APC kuma Uche Nnaji ne kaɗai ya fito takara a APC. Saboda haka idan Ekweremadu ya yi nasarar komawa APC, akwai yiwuwar ya yi takarar fidda gwani shi da Nnaji kenan.
Discussion about this post