Za muyi rashin marigayi Barnabas Bantex – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sanar da rasuwar tsohon mataimakin sa, Barnabas Bala Bantex a cikin wata doguwar sakon ta’aziyya da ya aika wa iyalan sa ranar Lahadi.

Bantext ya rasu ranar Lahadi, kamar yadda aka fidda sanarwar rasuwar sa.

El-Rufai ya bada tarihin marigayin tun daga lokacin da suka fara haduwa a jami’ar Ahmadu Bello a cikin 70’s.

” Tun a makaranta muna tare da Bantex, har muka gama. Sannan ko a ayyuka mun yi da yawa tare har na tsunduma ssiyasa. A nan ma muka yi takarar gwamna shi mataimakina tare kuma muka yi aiki tare har tsawon shekara huɗu.

El-Rufai ya kara da cewa marigayi Bantex mutumin kirki ne da jihar Kaduna za ta yi jimamin rashin sa.

Share.

game da Author