RASHIN TSARO YA DAGULE: An sace Sarki sukutum da iyalan sa 12 a Kaduna

0

Ƴan bindiga sun sun yi wa garin Kajuru shigar-kutse, su ka yi gaba da Sarkin Kajuru, Alhassan Adamu.

Sun ritsa basaraken na Karamar Hukumar Kajuru a gidan, su ka yi gaba da shi da kuma iyalan sa 12.

Cikin waɗanda aka sace ɗin har da mata da ƙananan yara.

Jikan Sarki Alasan, wanda kuma shi ne Ɗankajuru, mai suna Sa’idu Musa, ya shaida wa Daily Trust tabbacin garkuwar da aka yi da kakan na sa da kuma iyalan sa.

Ya ce lamarin ya faru kamar wajen 12:30 na Asabar da dare, wayewar yau Lahadi.

Ba a samu jin ta bakin Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Kaduna ba, Samuel Aruwan.

Haka shi ma Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Kaduna, Jagile Mohammed, bai ɗauki wayar kiran da aka yi masa ba.

Share.

game da Author