Jami’an Kwastam sun kama haramtattun kaya na miliyoyin naira a Katsina

0

Babban jami’in kwastam dake kula da yankin jihar Katsina Chedi Wada ya bayyana cewa hukumar ta kama haramtattun kaya na Naira miliyan 101,027,350 a wurare daban-daban a iyakokin shiga jihar.

Wada ya fadi haka wa manema labarai a makon jiya da yake nuna aiyukkan da hukumar ta yi tun bayan da ya karbi shugabancin hukumar a jihar watanni biyar da suka gabata.

Ya ce a cikin kayan da suka kama akwai mota kirar ‘Toyota Land Cruiser Prado Jeep’ wanda kudin ta ya kai naira miliyan 40, mota kirar ‘Toyota Hilux’ ita ma da ta kai naira miliyan 29, sannan da mota kirar marsandi wanda kudinta ya kai naira miliyan 4.

Wada ya ce akwai wasu motocin da hukumar ta kama da jimlar kudinsu ya kai Naira miliyan 91,592,500.00.

Ya Kuma ce hukumar ta kwace buhunan shikafa 225, jarkan man gyada 48, galan 8775 na man fetur, abincin dabobbi da Madara da jimlar kudinsu ya kai naira 9,434,850.00.

Bayan haka Wada ya yi kira ga mazauna kusa da iyakokin da su guji shiga cikin harkar fasakwauri domin idan aka kam su za su dandana kudar su.

Ya ce gwamnati ta bude boda hudu a kasar nan biyu a jihar Katsina sauran na Maigatari a jihar Jigawa da Illela a jihar Sokoto.

Tun bayan darewa kujerar mulkin Najeriya Gwamnatin Buhari ta saka kafar wando daya da masu fasakwari. Da farko dai shugaba Buhari ya datse iyakokin kasar nan ta yadda dole sai dai kabi ta inda doka ya ce, ko ka yi asara.

Share.

game da Author