Hukuncin Twitter akan Buhari: Taimako ne ga Buhari da Najeriya, Daga Ahmed Ilallah

0

Tozarcine ga Shugaba Buhari a kwatanta maganar sa da shugaban IPOB Nmendi Kanu.

Duk mai nazari akan hanyoyin sadarwa na zamani (social medias), musamman Twitter da WhatsApp yasan cewa danganta karsu da gwamnatin Najeriya akwai gargada.

Abun da ya faru na #EndSARS a 2020, Twitter taba da gudunmawa ta hanyar amfani da kafarta don Kamfen din #EndSARS, wanda aka samu miliyoyin twitte, Damar da Soshiyal Midiya suka bada, shi yasa zanga zangar tayi tasiri, taja hankalin duniya baki daya.

Twitter taki ta kafa Babbar Ofishinta a Najeriya, duk da miliyoyin masu amfani da kafar da suke dasu a kasar, yayin da ta gwammaci bude ofishin na Africa a kasar Ghana.

A yanzu ma ana dambarwa tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin WhatsApp, bisa sabon tsarin da kamfanin ya zo da shi, wanda tace zata rika bada bayanai masu amfani da kafarta ga uwar kamfaninta wato Facebook.

Twitter tayi bayani cewa, zata goge sokon ko wane shugaban a duniya, koma goge shafin sa idan har yayi amfani da kalaman da zu jawo hargitsi ga al’ummah, don mummunar fahimta da jama’ah suka yiwa sakon.

Goge sakon nin shugabannin ko goge shafin su ba sabon abu bane, haka ta faru ga tsohon shugaban USA Donald Trump.

Kafin rantsar da sabon shugaban kasar USA, ansa mu tarzoma a wurin wanda ya jawo cece-kuce, daga baya Trump yayi rubutu a shafinsa na Twitter “Ga wayanda suke tambaya. Ba zan halicci wurin ranrsuwa ba”.

Wannan kalamai inji Twitter, zai iya daukan fahimta daban daban a wajen jama’ah, kan iya zama dalili na tada hankali ga magoya bayansa.

Buhari, a matsayin sa na shugaba babbar kasa a Afirka, mai mutane sama da miliyan 200, kuma yana daga cikin fitattacen shugabannin duniya. Kalamun sa, za suyi tasiri ba kawai a Najeriya ba, ama duniya baki daya.

In har kalaman Buhari, zai iya haifar da hargitsi ga kasar mu, ko za ayi masa mummunar fahimta, kuma ya sabawa kaidodin Twitter, to hakan ba abin damuwa bane. Haka ta faru da shugaban kasar Brasil.

Kwatanta shugaba Buhari da Nnamdi Kanu, ko daidaita nauyin kalamun su, tabbas tozarcine ba ma kawai ga shi ba, harma Najeriya baki daya.

Anawa fahimtar, matsalolin da suka faru tsakin Najeriya da Twitter, su suka kara assasa wannan dambarwa tsakanin Twitter da Najeriya.

A wannan lokaci ne, Najeriya ta soma habbaka gina tattalin arziki na zamani wato (digital economy).

Irin wannan kamfanoni za suyi tasiri kwarai wajen habaka tattalin arzikin Najeriya.

Share.

game da Author