Akalla dalibai 13,000 ke shiga jami’o’in Amurka duk shekara

0

Jami’in hulda da jama’a a ofishin jakadancin kasar Amurka dake Najeriya Stephen Ibelli ya bayyana cewa duk shekara jami’o’in kasar na daukan dalibai ‘yan Najeriya akalla 13,000.

Ibelli ya fadi haka ne a taron kaddamar da manhaja mai taken ‘Windows on America’ Hub’ da aka yi a jami’ar Nnamdi Azikiwe NAU dake Awka jihar Anambra ranar Talata.

Ya ce an kirkiro manhajar ne domin taimaka wa daliban Jami’ar NAU dake sha’awar yin karatu a jam’o’in kasar Amurka.

“Ita wannan manhajan an samar da ita ne domin wayar da kan dalibai kan yadda a su yi karatu a lokacin da suke Amurka, yadda za su samu tallafi, yadda gwamnatin kasar ta ke, tarihi, al’adu da yadda makarantu suke a kasar, yadda ya kamata a rubuta CV wajen neman aiki da sauran su.

Ya ce duk horon da dalibai za su samu a wannan manhajar kyauta ne.

Ibelli ya yi kira ga dalibai da su rika amfani da wannan manhajar domin sanin abubuwan da basu sani game da Amurka da yadda za su samu damar yin karatu a kasar.

A nashi jawabin shugaban Jami’ar NAU Okechukwu Esimone ya ce Jami’ar NAU ta fara kokarin bude wannan manhajar tun a watan Disemba 2018.
Esimone ya ce sai a watan Yuli 2020 ne wannan magana ya tabbata har aka saka hannu a yarjejeniyar hin hakan.

Share.

game da Author