An gano malaman dake koyarwa a makarantun kudi kuma suna karbar albashi daga gwamnatin Kano

0

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta gano malamai akalla 3,268 dake koyarwa a makarantu masu zaman kansu kuma suna karbar albashi daga aljihun gwamnatin jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi na jihar Aliyu Yusuf ya sanar da haka ranar Talata a garin Kano.

Yusuf ya ce kwamitin da gwamnati ta kafa domin tantance malaman jihar ne ta bankado wadannan malamai kwanaki uku kafin a fara tantance malamai.

Ya ce kwamitin ta gano cewa wasu daga cikin malaman sun kai shekaru 10 wasu shekara 15 ko fiye suna karbar albashi daga asusun gwamnatin jihar amma kuma suna wata makarantar suna aiki, a can ma ana biyan su.

Sakamakon binciken kwamitin ya nuna cewa malaman na karbar albashi daga gwamnati kuma ita waccan makarantar da suke koyarwa na biyan su albashi, sannan har karo karatu suke yi ba tare da an sani ba.

Yusuf ya ce an samu wannan matsala ne a dalilin aikawa da malaman dake aiki da makarantun gwamnati zuwa makarantun dake zaman kansu saboda karancin malamai.

Ya yi kira ga mutane da su yi hakuri su daure domin gwamnati na kokarin inganta fannin ilimin a jihar ne shine ya sa za a ga jinkiri, amma da zarar ana kammala komai zai komo yadda yake.

Share.

game da Author