Gwamnatin Neja ta umarci ‘yan kwangila su dawo aiki duk da yaduwar Korona

0

Gwamnati jihar Neja ta umurci masu kwangilar aikin gine-gine a jihar su dawo su ci gaba da aiyukkan su duk da cewa jihar da kasar na fama da yaduwar annobar Covid-19.

Gwamnan jihar Abubakar Bello ya bada wannan umurnin da ya kai ziyaran gani da ido wasu hanyoyin da ake ginawa a babban birnin jihar, Minna.

Gwamna Bello ya ce bai kamata a dakatar da harkokin rayuwa ba saboda annobar Coronavirus ganin cewa fa babu wanda ya san ranar da za a rabu da ita a duniya ballantana jihar.

Hakan ya sa dole kawai gwamnati ta dawo harkokin mulki kawai a ci gaba da rayuwa.

Gwamnan ya yi kira ga masu aikin kwangilolin gine-gine a jihar cewa duk da an umarce su su dawo aiki, su tabbata suna bin ka’idojin da ak gindaya domin kauce wa kamuwa da cutar.

Ya ce gwamnati za ta kwace aikin duk dan kwangilan da bai kammala aikinsa ba kamar yadda yayi wa gwamnati alkawari. Sannan kuma ya yabawa kokarin da kamfanonin da ke aiki a jihar bisa maida hankali da suka yi tun a abaya.

Titin dake da nisan kilomita 4 a Moris da Tunga da aka bada kwangilar ginawa a shekaran 2017 akan Naira biliyan 2.4 na cikin hanyoyin da gwamnati ke kokarin ganin an kammala a jihar.

Share.

game da Author