Rahotanni daga London sun tabbatar da cewa an samu ‘yan wasa shida da cutar Coronavirus, bayan an yi wa ‘yan wasa da jami’ai 748 na kungiyoyi uku gwaji a ranakun Lahadi da Litinin.
Goal.com da sauran kafafen yada labarai na Ingila, sun ruwaito cewa an ki bayyana sunayen wadanda suka kamu da cutar saboda sabuwar yarjejeniyar da aka cimma cewa za a daina bayyana sunayen ‘yan wasan da suka kamu.
An dai same su da cutar ne bayan gwajin da ake ci gaba da yi wa kungiyoyi domin shirye-shiryen komawa karasa gasar Premier League ta 2019/2020 a ranar 1 Ga Yuni.
An dai gindaya ka’idar cewa sai an yi wa kowa gwaji tukunna.
‘Yan wasan shida da aka samu sun kamu da cutar dai an shawarce su kowa ya killace kan sa tsawon kwanaki shida.
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa za a koma wasan Premier League ranar 1 Ga Yuni.
Wasu bayanan shafuka 50 da Gwamnatin Ingila ta buga a ranar Litinin, sun nuna cewa za a koma ci gaba da gasar Premier League a ranar 1 Ga Yuni, 2020.
Bayanan da gwamnati ta buga sun nuna matakan da za a rika bi daya bayan daya wajen ci gaba da sake bude harkokin rayuwa da mu’amala a Ingila, tun bayan da annobar Coronavirus ta dagula duniya baki daya, har aka dakatar da komai, ciki har da wasannin kwallon kafa a duniya.
Mataki na biyu da Gwamnatin Boris Johnson ta gindaya, shi ne sake bude filayen kwallo domin a karasa gasar Premier League a kasar, amma ba tare da ‘yan kallo ko da mutum daya ba.
Sai dai kuma ana sa ran a cikin watan Yuli za a iya barin ‘yan kallo shiga kallon wasannin, saboda a tsare-tsaren bude harkoki a mataki na uku, za a sake bude gidajen sinimomi da gidajen aski da wankin gashi da kitso da sauran makamantan su.
“Amma kuma ba za a yi saurin bude wararen duk da aka san cinkoson mutane zai yi wahalar a bi doka da ka’idar kauce wa daukar cuta ba.”
“Gwamnati za ta ci gaba da duba irin ci gaba da nasarorin da ake samu a wasu kasashen da suka rigaya suka bude wasu wuraren gudanar da harkoki.
“Kuma gwamnati za ta kafa kwamitin bibiya da sa-ido da dubagaein yadda al’amurra ke gudana. Wannan kwamiti zai yi aiki kafada-da-kafada da dukkan bangaeorin da ke da ruwa da tsaki a wuraren kasuwanci da hada-hadar aka bude.”
Wannan bayani na gwamnati ya yi nuni da cewa ko da an kyale masu kallo su shiga filayen wasa nan gaba, to ba dafifi za a fara yi ba tukunna. Za a rika shiga ba da yawa ba, gwargwadon yadda aka ga cutar Coronavirus na raguwa, to sai a rika barin ‘yan kallo na kara yawa a sitadiyan kenan.
Ana ganin cewa karasa wasan zai ba Liverpool FC damar lashe kofin a ruwan sanyi, domin ta rigaya ta cinye ruwon, saura ta side kwano kawai, don kada kudaje su dame ta.
A wani labari mai kama da wannan kuma, kungiyar Atletico Madrid da ke Spain, ta bayyana cewa magoya bayan kungiyar 32 ne cutar Coronavirus ta kashe.
Sanarwar da kungiyar ta bayar, ta ce ba za ta sayar da lambobin tikitin su da suka saba saye ba a duk wasan da Atletico za ta yi a gida.
Atletico ta nuna takaicin mutuwar su, kasancewa ba su fashin kallon wasan kulob din.
A kan haka ta ce ba wanda zai zauna a kan kujerun su filin wasa har karshen wannan shekarar.