Mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu ya yi kira ga shugabanin kasashen Afrika da ECOWAS da su yi hatara da yin takatsantsan akan maganar aikawa da sojoji kasar Gambiya domin sasanta rikicin zaben shugaban Kasar da ya gudana a shekarar da ta wuce.
Ya ce idan aka bari har haka ya faru toh kasar za ta iya shiga cikin wata mawiyacin hali na rashin zaman lafiya da tashin hankali.
Daga karshe ya shawarci hukumomin kasar Gambiya da su yi kokarin kare yancin siyasar kasar da kokarin shawo kan matsalar kafin ya zama sanadiyyar tarwatsewar kasar.