Wata mazauniyar babban birnin tarayya Abuja mai suna Sandra kuma ‘yar shekara 29 ta gamu da ajalinta ne a babban asibitin ma’aikata na Abuja wato ‘Federal Staff Hospital’ saboda rashin kwararrun ma’aikatan da suka kula da ita a lokacin da aka kwantar da ita a asibitin.
Kanuwar marigayiyan mai suna Sophia ta fada ma wannan gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa Sandra dai ta tafi asibitinne tun lokacin da ta kamu da cutar yoyon fitsari da ya bukaci ayi mata aiki.
Amma garin yin wannan aikin ne likitocin suka yi kuskuren da ya kai ga mutuwarta.
Sophia ta ce likitocin sun fada wa Sandra cewa tana da kaban ciki da kuma wata laluran da ya shafi kodar ta.
Bayan an yi aikin an gama aka kuma sallame su zuwa gida Sandra dai bata kara samun lafiya ba. An sake mai da ita asibitin inda likitocin asibitin suka kara yi mata wani sabon aikin da ya huda huhunta kuma, daga nan dai bata sami sauki ba domin tun daga lokacin ciwo sai karuwa yake ta yi. Duk da haka likitocin basu fada wa ‘yan uwan Sandra cewa sun yi kuskuren huda mata huhu ba wanda ya sa madacin da ke cikinta ya daina aiki.
Koda suka sake komawa asibitin sai suka tarar asibitin na yajin aiki, ‘yan uwan suka roki alfarmar asibitin da ta basu wasikar komawa wata asibitin inda bayan sun kai ruwa rana da jami’an asibitin suka samu takardar da kyar.
Sophia ta ce nan da nan suka kai ta asibitin Nizamiya wato wata asibiti ne mallakar wasu ‘yan kasar Turkiyya, a nan ne likitocin suka fada wa ‘yan uwan Sandra a zahiri halin da take ciki sannan kuma suka ce sallamanta da rai zai yi wuya domin ta riga ta galabaita sannan idan har za’ a duba ta sai ta tanaji kudin da zai kai miliyan 6 zuwa 8, ‘yan uwan da kyar suka hada rabin kudin.
A binciken da muka gudanar bayan wannan mummunar abu da ya sami Sandra a wannan asibiti matar wani mai suna Pious tayi barin cikin da take da shi saboda wadansu magunguna zazzabi da malaman asibitin suka ba matarsa bayan sun san tana da ciki.
Haka kuma wani shima mai suna John ya rasa dansa wurin haihuwa a dalilin rashin ba matarsa kula da jaririn da su haifa a asibitin.
A dalilin irin wadannan korafe korafe ne Gidan jaridar Premium Times ta yi kokarin ta tatattauna da shugaban asibitin mai suna Chinwe Igwilo in da hakan ya ci tura saboda tafiya da akace wai shugaban asibitin tayi.
Daga karshe da muka tuntubi wani ma’aikacin asibitin ya fada ma wannan gidan Jarida PREMIUM TIMES cewa ba za su ce koma ba yanzu domin lauyoyin marigayiya Sandra sun tuntube su kuma kungiyar likitocin Najeriya na gudanar da bincike akan maganar.