Dalilin da ya sa mukayi ma shugabannin mu bore – Inji Mayakan Sojin Najeriya daga dajin Sambisa

0

Ko da yake Sojin Najeriya ta musanta rahoton da wannan gidan jarida PREMIUM TIMES tayi akan wahalar da sojojin suka yi ta fama dashi a dajin Sambisa, sai gashi a wata sabuwar Bidiyo ya nuna yadda sojojin suke nuna fushinsu akan abin da ya ke faruwa tsakaninsu da shugabanninsu a filin daga.

Bidiyon ya nuna cewa da gaske sojojin da suke filin daga a dajin Sambisa din sun nemi yin bore ga shugabanninsu bayan nuna rashinjin dadi da sukeyi a dajin.

Acikin sabon bidiyon ya nuna wani babban jami’in Soja a tsaye yana sauraran korafe korafen da sojojin sukeyi.
A madadin sojojin daya daga cikinsu yayi ma shugaban nasu bayani akan abubuwan da yake damun sojojin.

Ya ce rashin wadataccen abinci, ruwan sha da ingantattun kayan aiki sune suke kawo musu Matsala a aikinsu. Bayan haka kuma ya yi bayanin rashin abin hawa da sukayi ta fama dashi da yadda sai sun taka su ke zuwa duk ida za su domin motocinsu sun lalace sannan bindigogin da suke amfani dasu duk sun sami matsaloli da bam dabam.

Sannan ya yi kuka da yadda shugabannin nasu basa gaya musu gaskiya akan ainihin al’amura musamman wadanda suka shafi aikin nasu a wancan lokaci sannan yace kafin su sami izinin tafiya gida wurin iyalensu sai sun yi hargitsi tsakaninsu da shugabannin nasu.

Duk da wadannan matsaloli da aka samu a lokacin arangamar da Boko Haram yanzu dai sojojin Najeriya ta samu nasaran dakile maboyar kungiyar in da ta kwato babbabn maboyarsu da ke dajin Sambisa wato (Camp Zero).

Share.

game da Author