Lauyan shugaban kasar Gambiya Edu Gomez ya shawarci shugaban kasar Yahya Jammeh da ya sauka daga kan karagar mulkin Kasar.
Lauyan yafadi hakanne a daidai yana mika takardan ajiye aikinsa sannan ya fice daga kasar zuwa Senegal.
Gomez ne ya jagoranci jam’iyar APRC da su ka shigar da kara akan rashin amincewa da sakamakon zaben kasar kotu.
Kasar Najeriya ta aika jiragen yaki da sojoji 200 domin haduwa da na kasar Senegal akan shiri da akeyi na tunkarar kasar Gambiya muddun shugaban kasar Yahya Jammeh bai hakura ya Sauka da ga kan karagar mulkin kasar Gambiya ba.
Kasashen da ke hadaddiyar Kungiyar hadin kai da cinikaiya na kasashen Afrika ta yamma, ECOWAS sun gama shiri domin ganin an tsige Yahya Jammeh ko da karfin tuwo ne.
Tuni zababben shugaban kasar Adama Barrow ya bar kasar zuwa kasar Senegal bayan kin amincewa da shugaban kasar Yahya Jammeh yayi akan ya hakura ya ajiye mulkin tunda ya fadi zaben da akayi a kasar.
Yau ne mataimakin shugaban kasar ya sauka daga kujeransa.