Gwamnar jihar Borno Kashim Shettima yace hadarin jirgin saman sojin Najeriya da ya auku a sansanin yan gudun hijira a garin Ran cikin kuskure ya tada ma gwamnatin jihar hankali.
Shettima yace dama idan har ana yaki toh fa dole a samu irin wadannan hadararruka.
Gidan jaridar Premium Times ta rahotan cewa akalla mutane 52 suka rasa rayukansu sannan kuma mutane 120 ne suka sami raunuka dabam dabam.
Gwamna Shettima ya ce kamar yadda tarihi na yaki ya nuna irin wadannan hadarorrika yakan faru musamman wanda ya shafi mutanen da basuji ba basu sha ba.
Gwamnan ya fadi hakan ne yayin da wakilan gwamnatin tarayya suka kawo masa ziyara domin jajanta masa da iyalan wadanda abin ya faru dasu.
Ya ce a gaskiya abinda ya faru babu dadi amma kuma sojojin Najeriya sun burge yadda basu boye abin da ya faruba, domin da ba haka aka yi ba mutane za su zargeni da hannu acikin aikata wannan aikin.
Ya nuna godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman yadda ya nuna jaruntarsa wajen ganin an kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram.
Bayan haka jagoran wakilan shugaban kasa da suka ziyarci jihar Borno ne din kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari yace tabbas hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi matka sannan kuma yana tabbatar wa jihar cewa gwamnati za ta kara dagewa domin ta ga Kungiyar Boko Haram ya zamo tarihi a kasa Najeriya.
Wakilan sun ziyarci fadar sarkin Dikwa Shehu Dikwa wanda a masarautarsa ne aka samu wannan hadari, bayan haka kuma sun ziyarci ofishin Red Cross, da asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri domin ganin wadanda aka kwantar sanadiyar hadarin.