Shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh yace ba zai sauka daga shugabancin kasar Gambiya ba sai kotun kasar ta saurari karar da suka shigar.
Jammeh yace jam’iyyar sa ta kai kara babbar kotun kasar domin ta dakatar da rantsar da Adama Barrow saboda wadansu dalilai da ta lissafa.
Ganin cewa babban mai shari’ar kasar Emmanuel Fabenle ya na daya daga cikin wadanda ke cikin karar da aka shigar in da ba zai iya sauraren karar ba dole alkalai daga Najeriya su zo domin sauraren karan da yanke hukunci akai.
Jammeh yace ya na tabbatar ma shugabannin ECOWAS cewa idan har aka bi hakan kamar yadda dokar kasar ta gindaya toh a shirye yake da ya bi duk abin da kotu yanke akai.
Yahya Jammeh ya fadi hakanne a wata hirar wayan tafi da gidanka da yayi da shugaban kasar Liberiya akan abinda ya fi ganin ya dace Kenan ayi mai makon shirin da sukeyi na afka masa.
Yace dokar kasar sa ta bashi ikon ya shigar da kara kuma a saurari karan. Kuma jam’iyyarsa ta shigar da kara saboda haka dole ne a saurare ta kafin a rantsar da sabuwar gwamnati.