Mafi yawan ‘yan Najeriya sun yi na’am da yin amfani da dabarun ba da tazaran haihuwa

0

A wata bincike da akayi a shekara ta 2015 akan ba da tazaran haihuwa ya nuna cewa yawa yawan matan da suke amfani da dabarun ba da tazaran iyali ya karu matuka.

A binciken da hukumar Kididdiga wato ‘National Bureau of Statistics’ ta yi a kwanakinna ya nuna cewa a shekaran 2014 kashi 23 ne cikin 100 na mata ke amfani da dabarun in da a shekarar 2015 ya karu inda ya kai kashi 30 bisa 100.

Gidan jaridar PREMIUM TIMES ta tattauna da wadansu magidanta da Mata akan yadda suke amfani da dabarun kayyade iyalin.

Wata mazauniyar garin Abuja Aisha Jamiu ta ce hakika tasan mene ne ake nufi da dabarun ba da tazaran haihuwa kuma tana amfani dashi domin ta bada tazara a haihuwarta.

Ita kuma Janet Asumu ma’aikaciyar gwamnati ce ta lallai ta tsorata da maganganun da mata su ke gaya mata akan matsalolin da sukan gamu da shi a lokacin da suke amfani da dabarun saboda haka ne ya sa take amfani da dabarun gargajiya kamar kirga kwanakin ganin al’adarta, amfani da wasu sauyoyin itatuwa, zubar da maniyi a waje da maza kan yi a lokacin saduwa da dai sauran su.

Janet Asumu ta ce daga baya ta amince da dabarun na asibiti bayan bayanai akai da wata malamar asibiti tayi mata lokacin da ta tafi awon haihuwar danta na uku.

Lara Nwosu ta ce bata so ta yi amfani da dabarun ba da tazarran haihuwa ba amma kuma ganin cewa maigidanta ba mai son ‘ya’ya da yawa ba ne shine yasa ta karbi abin hannu bibbiyu.

Malama Lara ta ce ta yi amfani da dabarar ashanar hannu wato ‘inplants’bayan ta yi shawara da likitanta a asibiti, duk da haka bai hana ta daukan ciki ba domin yanzu haka ‘ya’yanta 3 kuma ta kasa gane dalilin da ya sa dabaran bai yi mata ba.

Da yake ba da bayanai akan wash dalilan da ya sa wasu dabarun basa yi musu ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce hakan na faruwa ne idan mace bata yi amfani da dabarar da ta zaba ba yadda ya kamata domin dabarun iri-iri ne kuma ya shawarci mata da su je agwada jininsu kafin su fara amfani da dabarun domin abin jini jin ne.

Wani limamin ikilisiyar Living Faith wanda ba ya so a fadi sunansa ya ce a ra’ayinsa ya dace ma’aurata su haifi ‘ya’yan da za su iya kulawa da su ba tare da sun wahalaba amma ba zai shawarci mabiyansa da suyi amfani da magani wajen kayyade iyali ba saboda bai amince da hakan ba.

Share.

game da Author