Katafaren kantin zamani da ke Kano, BARAKAT STORES ya aika wa Babban Kamandan Bataliyar Sojoji ta 3 da ke Barikin Bukavu wasiƙar godiya, bisa ƙoƙarin da sojoji suka yi wajen ƙwato wasu kayayyakin kantin daga hannun ɓatagari, waɗanda suka fasa kantin suka kwashe kayayyaki.
Cikin wasiƙar wadda Babban Manajan kantin mai suna Muhammad Sani ya sa wa hannu a ranar 2 ga Agusta, washegarin ranar da lamarin ya faru, Sani ya nuna godiya dangane da saurin kai ɗaukin da sojoji suka yi. Kuma ya gode wa sauran jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda, sibil defen da sauran mutanen gari, waɗanda suka taimaka aka ƙwato wasu kayayyakin daga hannun masu kiran kan su ‘yan kwasar ‘ganima.’
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka fasa kantin, aka riƙa jidar kayayyaki, kuma an nuno bidiyon matasa na jidar jarkokin man girki.
Sai dai kuma wani bidiyo da aka nuno matashi ya fizgi jarkar man girki daga kan motar sojoji, ya sa wasu sun riƙa yaɗa cewa su ma sojojin ko sun shiga cikin zugar ‘yan kwasar ganima ne. Lamarin da Rundunar Sojojin Najeriya ta ƙaryata.
Sojoji sun yi ƙarin bayani kan jarkar mai wadda ɗan zanga-zanga a fizge daga cikin motar sojoji a Kano.
Rundunar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta fitar da sanarwar ƙarin haske inda ta ƙaryata zargin da wasu suka riƙa yaɗawa wai sojoji sun shiga sahun ‘yan ‘kwasar ganima’ a Kano, a yayin zanga-zanga.
Kakakin Yaɗa Labaran Sojoji, Onyema Nwachukwu ya yi magana dangane da wani guntun bidiyo da aka riƙa yaɗawa, kuma ya gane duniya, inda aka nuno wani matashi ya bi motar sojoji ta na gudu shi kuma ya fizgi jarkar mai daga cikin lodin jarkokin mai da ke kan motar.
A bidiyon dai an nuno buɗaɗɗiyar motar sojoji ɗauke da harkokin mai ta na ƙoƙarin ficewa a guje daga cikin masu zanga-zanga, yayin da masu zanga-zanga ke kwasar ganima a Barakat Super Market, da ke kan Titin State Road, Kano, a ranar Alhamis.
Nwachuku ya ce abin da ya faru shi ne wasu ɓatagari sun fasa kantin su na kwasar kayayyakin da ke ciki, kafin sojoji su je wurin.
“To sojoji na isa sai suka ƙwace jarjokin man girki da kayyaki daga hannun wasu masu zanga-zanga.
Ya ce su na kan hanyar su ta maida kayan ne a kantin, sai akayi masu kiran gaggawa, “aka ce su hanzarta su kai ɗauki a Gidan Gwamnatin Kano, domin masu zanga-zanga na ƙoƙarin afkawa cikin gidan.”
Nwachuku ya ce yayin da motar sojojin ke ƙoƙarin komawa zuwa gidan Gwamnatin Kano da ke kusa da kantin ne, wani ɗan zanga-zanga ya bi motar har ya fizgi jarkar man girki ɗaya. Amma ba kwasar ‘ganima’ sojoji suka yi suka nemi gudu kamar yadda wasu suka riƙa yaɗawa ba.
Sojojin Najeriya sun nuna yadda sojojin na Kano suka maida kayan ga Manajan Barakat Stores, kuma sun nuna wasiƙar godiya da manajan ya rubuta wa sojojin.
Discussion about this post