Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta bankaɗo ‘yan Najeriya da ke zaune ƙasashen waje, waɗanda ta ce su ne suka ɗauki nauyin shirya zanga-zangar da ake yi tun daga ranar Alhamis.
Haka kuma gwamnatin ta ce ta kafa masu idanun bibiyar duk wani taku da suka yi, baya ga kulle asusun bankunan su da ta yi.
Shugaban Hukumar Shige da Fice na Ƙasa, Kemi Nandap ya ce waɗanda suka ɗauki nauyin shirya zanga-zangar za a damƙe su da zarar sun jefo ƙafar su cikin Najeriya.
Nandap ya bayyana haka a ranar Talata, a Abuja, lokacin taron manema labarai na haɗa-ka da ɓangarorin jami’an tsaron Najeriya suka gabatar, a Hedikwatar Tsaron Najeriya.
Ta ce, “mun gano wasu ‘yan Najeriya mazauna waje da suka ɗauki nauyin zanga-zanga; an sa su a jerin waɗanda ake jiran shigowar su Najeriya a yi cacukui da su.
“Duk lokacin da suka sake suka shigo Najeriya, za a sanar da mu, kuma za a damƙe su a miƙa su hannun hukumar da ta dace.”
Ta ce jami’an ta da dama an girke su a kan iyakoki na ƙasa da na ruwa da filayen jiragen sama, domin su tabbatar da samar da kyakkyawan tsaro da sa-ido kan hanyoyin shigowa Najeriya.
Kuma ta ƙara da cewa Hukumar NIS ta ƙara sa ido sosai wajen ganin an a hana wata ƙasar waje yi wa Najeriya kutse.
Dama Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya ce sun gano masu ɗaukar nauyin zanga-zanga, amma bai yi wani ƙarin bayani ba.
Ya ce an kulle asusun bankunan su, “kuma yawancin su duk a ƙasashen waje suke zaune.”
Discussion about this post