A ci gaba da zanga-zanga yau Litinin, rana ta 5 a Legas, dandazon masu zanga-zanga sun yi kira da a gaggauta tsige Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun.
Neman cire shi ɗin ya biyo bayan rahotanni da bidiyoyin da ake watsawa a soshiyal midiya da ke nuno yadda ‘yan sandan Najeriya ke kashe masu zanga-zanga.
Sai dai duk da haka Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya ce jami’an sa ba su kashe ko kaza ba.
Egbetokun dai ya kamata a ce ya yi ritaya daga aiki a cikin wannan wata na Agusta. To amma akwai yiwuwar ya zarce zuwa bayan zaɓen 2027, bisa la’akari da ƙarin wa’adin da Tinubu ya nemi a yi wa Sufeto Janar su riƙa yin shekaru biyar kan aiki.
Rahotanni da dama sun tabbatar da yadda ‘yan sanda suka bindige masu zanga-zanga da dama a garuruwa daban-daban. Kamar a Kano, Bauchi, Neja, Abuja, Katsina da garuruwa daban-daban.
Cikin waɗanda suka ji wa ciwo har da wakilin PREMIUM TIMES, Yakubu Mohammed, wanda aka buga da gindin bindiga a Abuja.
Haka kuma wani wakilin namu ‘yan sanda sun ratattake motar sa da harbin albarusai.
Masu zanga-zanga ɗin a Legas sun kuma yi fatali da ƙarin mafi ƙanƙantar albashi na Naira 70,000 da Shugaban Ƙasa ya sa wa hannu.
Batun janye zanga-zangar da Tinubu ya yi roƙo kuwa, wani ɗan zanga-zanga ya ce, “Ai ba da Fadar Aso Rock aka shirya zanga-zanga ba. Don haka ba daga can za a tsara mana yadda za mu daina ba.”
An dai shirya zanga-zanga ce daga ranar 1 zuwa 10 ga Agusta.
Discussion about this post