Kotun tafi-da-gidan-ka a Kano ta tura waɗanda ake zargi da tayar da tarzoma su 632 zuwa kurkuku.
Kotun ta zarge su da laifin ɓarnata dukiyoyin jama’a da na gwamnati a yayin zanga-zanga.
Sauran canje-canjen da ake yi masu sun haɗa da haɗa baki a aikata laifuka, satar kayayyaki, haɗuwa su taru ba bisa doka ba, haddasa rigima, shiga wuraren da ba na su ba, kuma ba da labarin izni ba, sai kuma banka wa wurare wuta.
Babban Mai Shari’a a Kotun Majistare, Ibrahim Mansur-Yola, Hadiza Rabi’u Bello da Abba Muttaƙa Ɗandago ne suka shugabanci kotunan.
Kotun ta ɗage zaman zuwa ranar 19 ga Agusta domin fara sauraren ƙarar da aka shigar kan su.
Daraktan Gabatar da Ƙararraki na Jihar Kano, Salisu Tahir, ya shaida wa kotu cewa waɗanda ake zargin duk sun aikata laifukan ne a ranar Alhamis, 1 ga Agusta.
Ita dai Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ‘masu tayar da tarzoma 873 muka kama, ba masu zanga-zanga ba’.
Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce jami’an su sun samu nasarar kama masu tayar da tarzomar ɓarnata dukiyoyi da kwasar kayayyaki a lokacin zanga-zanga.
Ya bayyana hakan ne a lokacin taron wata-wata na jami’an tsaro, wanda Kwamitin Haɗin Guiwar Tsare-tsaren Tsaro Tsakanin Hukumomin Tsaro (SCIPC) ya shirya a Hedikwatar DSS a ranar Litinin, a Abuja.
Ya ce akwai bambanci sosai tsakanin masu zanga-zanga da masu tada tarzoma.
Adejobi ya ce yayin da aka samu zanga-zangar lumana a wasu jihohi, a wasu wurare kuwa masu tarzoma ne da ɓatagari suka fito suka yi ɓarna.
“Saboda haka kama waɗanda suka yi tarzoma ba kama masu zanga-zanga ba ne. Zanga-zanga daban, masu tayar da tarzoma kuma daban.
“Na tabbatar ku na sane da cewa wasu gwamnoni sun kusance su.
“Ai za ka kusanci dandazon mutane ne masu zanga-zangar lumana, ba masu ɗauke da duwatsu da sauran muggan makamai ba.”
Ya yaba dangane da yadda ‘yan sanda, sojoji da sauran jami’an tsaro suka kula da yadda aka tafiyar da zanga-zanga.
Ya ce masu zanga-zanga a Abuja sun karya umarnin hukumcin kotu, wadda ta ce su tsaya iyakar cikin filin wasa na Mashood Abiola kaɗai.
Ya ce kasancewar ‘yan sanda a wurin zanga-zanga ba don su ci zarafin kowa ba ne sai don su kare rayuka da dukiyoyin gwamnati.
Ya ce an killace Dandalin Eagle Square ne domin a kare Fadar Shugaban Ƙasa, Majalisa da Ofisoshin Gwamnantin Tarayya da ke zagayen wurin.
“To ina tabbatar maku waɗanda aka kama a faɗin ƙasar nan ba masu zanga-zanga ba ne, masu tarzoma ne da suka riƙa lalata dukiyoyi da kwasar kayayyaki.
“Saboda haka ba na son muna amfani da kalmar an kama masu zanga-zanga. Domin masu tayar da tarzoma muka kama.
“Kuma mun kama masu tarzoma su 873 a faɗin ƙasar nan, dukkan su sun aikata laifuka ne yayin fakewa da zanga-zanga, suka tayar da tarzoma.” Inji shi.
Ya ce an kuma kama wasu ɗaiɗaikun mutane da suka aikata laifin cin amanar ƙasa, inda suka riƙa filfita tutocin wata ƙasar waje a cikin Najeriya.
Ya ce sun kama teloli masu ɗinka tutocin Rasha a Kano da Kaduna.
Discussion about this post