Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, ya bayyana cewa yanayin da Jam’iyyar APC ke mulki karkashin shugaban Bola Tinubu, ko haufi ba shi da shi cewa PDP za ta kwace mulki a 2027.
Gwamna Bala Ya kara da cewa, za su yo hayar tinubu da kan sa ya zo ya yi wa jam’iyyar Darektan kamfen a lokacin kamfen na 2027.
Sannan kuma ya bayyana zanga-zangar da ta ɓarke a faɗin ƙasar nan, ishara ce da kuma hannun-ka-mai-sanda ga shugabannin Arewa, wadda za su yi amfani da ita su shiga taitayin yi wa jama’a aiki wurjanjan.
Bala ya bayyana haka yayin da yake jawabi wajen ƙaddamar da kamfen ɗin PDP domin tunkarar zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Bauchi.
Da yake magana kan jawabin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan masu zanga-zanga, Gwamnan Bauchi ya ce surutai kawai ya yi marasa ma’ana, waɗanda ba su taɓo gundarin ainihin matsalolin da suka dabaibaye ƙasar nan ba.
Ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta daina bai wa ‘yan Najeriya dalilai marasa kan-gado kuma ta daina neman a yi mata uziri, ta gaggauta magance ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya.
“Wannan zanga-zanga dai ta koya mana abubuwa da yawa da darussan da suka kamata mu koya. Amma ita gwamnatin APC ba ta ɗauki darasin komai ba.” Inji gwamnan.
“Ma saurari jawabin Shugaban Ƙasa a cikin natsuwa, kuma na fahimci bai ce komai ba sai surutai ratatata marasa kan-gado.
“Bai ma yarda ana fama da matsalolin da suka addabi ƙasar nan ba. Bai taɓo ainihin matsalolin ba.
“Ban ce shi kaɗai ke da laifi na. Laidin mu ne daga shi har mu a jihohi kuwa ƙananan hukumomi.
“A Arewa dai wannan zanga-zangar hannun ka mai sanda ce ga shugabanni, domin su tashi su yi wa al’umma ayyuka nagari da suka dace a cikin kyakkyawan shugabanci da mutunta jama’a.”
Gwamna Bala Mohammed ya nuna damuwa sosai kan tsananin yunwa a ƙasar nan, tare da cewa gwamnatin tarayya ba ta yin hoɓɓasa da ƙoƙarin da ya dace ta riƙa yi.
“Mun ji wasu ministoci na surutai wai an raba wa gwamnoni tirelolin abinci 70 ko Naira miliyan 500 mene ne. Shin ita gwamnatin tarayya nawa take samu, kuma me da me ta yi da kuɗaɗen?”
Discussion about this post