Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama wasu matasa 39 da ake zargi batagari ne da suka rika fasa shaguna da satar kayan gwamnati lokacin Zanga-Zanga.
Kakakin rundunar Mansir Hassan ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar Litini a garin Kaduna.
“Rundunar ta kama matasa da suka rika sata da sunan ganima a lokacin zanga-zangar.
Hassan ya ce wadannan mutane da suka kama na dauke da tutar kasashen Chana da Rasha sannan sun ta fasa gine-ginen mutane da na gwamnati.
“Mota kirar Hilux na KADVS, Toyota Yaris na wani dan jarida, da Ofishin KASTLEA dake Zone 6 a Zaria na daga cikin kayan da mstasan suka kona a lokacin zanga-zangar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Audu Dabigi ya yaba kokarin jami’an tsaro a lokacin kwantar da tarzoman.
Dabigi ya yi kira ga mutane da su kiyaye dokar hana walwala da gwamnati ta saka yana mai cewa duk wanda aka kama da laifin saba wa dokar za a kama shi kuma a hukunta shi bisa ga doka.
Bayan haka kakakin rundunar Hassan ya karyata labarin kwace mortar Yaki na rundunar ‘Armored Personnel Carrier (APC)’ da masu zanga-zanga suka yi a jihar.
Hassan ya ce Motar ta ‘yan sanda ne amma ba kwace shi masu zanga-zanga suka yi ba. Yan sanda na cikin motar take ta shawage da su matasan domin a lokacin idan ba haka aka yi ba zai kai ga an rasa rayuka.
Discussion about this post