Kwamishinan tsaron Jihar Kaduna Samiel Aruwan ya ƙaruata raɗeraɗin da ake ta yaɗawa a shfukan yanar gizo, cewa an sassata tsaeon awowin dokar hana walwala na awa 24 da gwamnatin jihar ta saka.
A wata sanarwa da ya ska wa hannu ranar Laraba, Aruwan ya ce Sam babu wannan magana, sannan ya hori jama’ a da su cigaba da bin doka da oda domin ƙauce wa afka wa cikin halin da na sani.
Ya ce ” Doka fa na nan daram, ba a cire ta ba sannan ba a sassauta taba. Kowa ya bi doka don ya zauna lafiya.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mansir Hassan ya ce sun kama wani mai garkuwa da mutanen da makamai a jihar
Hassan ya ce dakarun sun kama Abdulrahman mazaunin Karshi, Abuja da bindiga kirar AK-47 daya da harsasai 27.
Ya ce bayan ya shiga hannun jami’an tsaro Abdulrahman ya ce yana daga cikin mutanen da suka rika garkuwa da mutanen a Ikara jihar Kaduna.
Hassan ya ce da zaran sun kammala bincike za su kai Abdulrahman kotu domin yanke masa hukunci.
Discussion about this post