A wani ƙazamin faɗan kura-ta-ci-kura da aka yi tsakanin sansanin gogarma Bello Ƙaura da yaran Hatsabibi Halilu Sububu, an tabbatar da kashe masu haƙar ma’adinai da dama, waɗanda faɗan ya ritsa da su a dajin da ake haƙar wa Halilu Sububu ma’adinai, cikin Jihar Zamfara.
Wannan batarnaƙar batakashi ta faru ne ranar Asabar wajen ƙarfe 4 na yamma a dajin Bagega da Sunke a cikin Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara.
Wani ganau kuma wanda faɗan ya ritsa da shi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa yaran Bello Ƙaura ne suka yi wa wurin haƙar ma’adinan na Halilu Sububu tattakin dirar-mikiya, inda su na isa suka fara buɗe wuta kan masu haƙar ma’adinai da kuma ‘yan bindiga yaran Sububu da ke gadin wurin.
Shi dai gogarma Sububu shi ke mallakar akasarin wuraren haƙar ma’adinai da ke yankin Bagega da Sunke a Ƙaramar Hukumar Anka.
Cikin ‘yan shekarun nan, Halilu Sububu wanda tantirin gogarman ɗan bindiga ne, wanda a baya ya shahara sosai wajen safarar muggan makamai daga maƙwabtan ƙasashe zuwa yankin Sokoto da Zamfara, a yanzu ya fi maida hankali kacokan kan harkar haƙar ma’adinai a fafareren dajin ya da tashi daga Anka har ya nausa yankin Maru zuwa Tsafe, duk a cikin Jihar Zamfara.
Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar cewa Sububu na ɗaukar ƙarti matasa majiya ƙarfi da matasa su na yi masa aikin haƙar ma’adinai, kuma har da zinari.
Ya mamaye ƙauyukan yammaci da gabacin Anka, waɗanda ya yi wa alƙawarin ba su kariya daga hare-haren wasu ‘yan bindiga, muddin suka ba shi haɗin kai ya ci gaba da haƙar ma’adinai.
Sububu, wanda ake kira Buzu dai ya na da alaƙa ta kusanci sosai da ‘yan ta’adda mayaƙan ‘jihadi’ da jidali a Jamhuriyar Nijar, Mali, Libya da Burkina Faso. Kuma gazagurun mai safarar muggan makamai ne, har da irin su babbar bindigar nan RPG, wato tashi-gari-barde.
Tuni dai Rundunar Sojojin Najeriya ta ayyana shi a matsayin ɗan ta’addar da take nema ruwa a jallo, amma har yau ba a kam masa ba.
Farmakin Kura-ta-ci-kura:
Wani mazaunin ƙauyen Dareta, mai suna Isa Dareta, ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa an fafata kusan tsawon sa’a ɗaya a harin da yaran Bello Ƙaura suka kai kan sansanin haƙar ma’adinai mallakar Halilu Sububu.
“Wurin haƙar ma’adinan ya na gefen ƙauyen Ɗan Kamfani, kuma duk wuraren mallakar Halilu Sububu ne, wato Buzu,” inji majiyar.
“Yaran Bello Ƙaura sun kai samame wajen ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar. Kuma Bello Ƙaura ɗin da kan sa ne ya jagoranci kai harin, inda ya je ya na neman Halilu Sububu.”
Dareta ya ce ‘yan ta’addar ko da suka hango mutane na ta aikin haƙar ma’adinai a cikin ramu, sai suka fara antayo masu zabarin harbi da bindigogi ba ƙaƙƙautawa.
“Wuta ta yi wuta har wani rami ya rufta, amma an yi sa’a babu kowa a ciki,” cewar majiyar wakilin mu.
Yayin da suka fara buɗe wuta, sai wasu tsirarun ‘yan bindiga yaran Sububu da ke gadin wurin haƙar ma’adinan suka fara musayar wuta da su Bello Ƙaura. Amma saboda an fi su yawa, tilas suka ja baya.
Yaran Sububu masu gadin wurin sun tsere da bindigogin su, amma fa sun bar baburan su a wurin da kuma gawarwakin masu haƙar ma’adinai ɗin da aka bindige.
Dareta wanda ke zaune a ƙauyen kusa da Ɗan Kamfani, ya ce lallai Bello Ƙaura ya je ne musamman domin yin arba da Sububu, su yi ta ta ƙare.
To sai dai kuma wani mai haƙar ma’adinai da ke wa Sububu aiki, a wurare da yawa, ya ce su Ƙaura sun je ne kai wa mutanen da ke aikin haƙar ma’adinai hari ne kawai.
“Ai kowa ya san Halilu ba ya zama da dajin Ɗan Kamfani inda ake haƙo masa ma’adinai. Ya na da ƙaƙƙarfan sansani a wajen garin Bagega, inda yake zaune lafiya shi da mutanen yankin.”
Haka mai haƙar ma’adinan ya shaida wa wakilin mu, amma ya ce a sakaya sunan sa, don kada a biyo daga baya a sakaya shi.
“Bello Ƙaura ya san Halilu Sububu ba ya zaune wurin. Da yana wurin zaune ai Bello Ƙaura bai isa ya je wurin ba. Ba ma zai ko yi tunanin kama hanya ba.”
Wasu majiyoyi biyu, ciki har da wani cikin dattawan shiyyar Fulani na wajen sun shaida wa wakilin mu cewa Sububu ya na cikin Ƙaramar Hukumar Maradun a lokacin da aka kai wa sansanin haƙar ma’adinan sa hari.
“Kuma ni dai ba zan iya sanin adadin mutane nawa aka kashe ba, amma dai da ido na na ga gawarwaki bakwai a kwance bayan da aka daina harbe-harben.” Cewar Dareta.
Sububu da Ƙaura sun daɗe su na gaba da juna tsakanin su. Amma dai wannan lokacin ne gaggan biyu suka fara yin gumurzu.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Sububu shi ne ɗan bindigar da ya fara mallakar wuraren haƙar ma’adinai.
Ya bar sansanin sa na Sububu ta Jihar Sokoto ya koma a Bagega, ƙauyen da ke hada-hadar kasuwanci tsanakin mutanen yankin Anka da Maru.
Lokacin da Sububu ya fara haƙar ma’adinai a Ɗan Kamfani, babu wani ɗan ta’adda da ya yi amanna cewa harkar ma’adinai ta na da fa’idar samun ƙazaman kuɗi ba.
“Amma lokacin da ya fara samun miliyoyin kuɗaɗe, sai wasu da dama a cikin ‘yan bindigar suka fara mamaye wasu ramukan da ke can nesa da daya na Halilu Sububu.
Majiya da masana duk sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindiga sun karkata wajen haƙar ma’adinai, saboda yanzu harkar garkuwa da mutane da fashi ba su kawo kuɗi sosai kamar harkar hada-hadar ma’adinai.
Discussion about this post