Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa akwai buƙatar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yarda da cewa ta tafka kura-kurai a tsare-tsare da fasalin tattalin arzikin ƙasa wanda ta bijiro da shi, daga nan kuma sai ta sake bijiro da wasu tsare-tsaren da za su iya kai ƙasar nan gaci, kuma su sauƙaƙe tsadar rayuwa da ake ta gaganiya kan ta a faɗin ƙasar nan.
Shekarau wanda tsohon Ministan Ilmi ne, kuma ya yi sanata tsakanin 2019 zuwa 2023, ya ce domin shawo kan halin da ƙasar nan ta afka akwai matsananciyar buƙatar Tinubu da majiɓintan gwamnatin sa su sake nazarin tsare-tsaren tattalin arzikin da zai fitar da ƙasar nan daga ƙuncin da ake fama da shi.
“Kamar yadda a tsarin koyarwa ake cewa, mafi sauƙin hanyar fahimta da koyon darasi shi ne mutum ya gane irin kura-kuran da ya tafka,” haka Shekarau ya furta yayin tattaunawa da shi a Gidan Talabijin na Channels, a ranar Juma’a.
“Gwamnati ta zauna ta sake tilawar wuraren da ta tafka kuskure. Shin waɗanne tsare-tsare ne aka bijiro da su har suka afka ƙasar nan cikin masifar yunwa da tsadar rayuwar da ta cilla malejin tsadar abinci sama zuwa kashi 40% bisa 100%?”
Masifar raɗaɗin tsadar rayuwa ya afka wa ‘yan Najeriya tun daga ranar da Tinubu ya janye tallafin fetur, sannan kuma aka ƙara ruruta taɓarɓarewar tattalin arziki ta hanyar sakin Naira tsakiyar kasuwa domin ta ƙwaci kan ta daga hannun Dala, a kokawar da ba ta da ƙafafun tsayuwar da za a yi gwagwagwa da ita.
Discussion about this post