Mata masu zaman kansu a Kano sun koka da rashin Kwastomomi saboda dokar hana walwala da aka saka a faɗin jihar.
Sun roƙi masu zanga-zanga su yi haƙuri su janye zanga-zangar da suke yi, su koma teburin tattaunawa da gwamnati maimakon tituna da suke fitowa.
Sun shaida cewa rashin Kwastomomi ya sa rayuwa ta yi musu tsada a cikin ƴan kwanakin da aka saka dokar.
” Kwana biyu kenan a jere ban ci abinci ba saboda Kwastomomi na su zo ba saboda dokar hana walwala, da babu da sun leƙo na ɗan samu kuɗin abinci.
” Ni fa har da haɗa harkar da zan samu N30,000 da wasu kwastomomi, amma wannan doka ya hana su zuwa, gaskiya an ɓata min harka saboda doka.
” Wani mai siyar da kan Akuya wa gidajen cin abinci ya koka cewa babu kasuwa saboda dokar hana walwala.
Duka matan da suka tattauna da NAN sun ce an kira musu ruwa ne kawai ƴan zanga-zanga’ suka yi amma sun jefa su cikin halin ƙaƙanikayi saboda dokar hana walwala da gwamnati ta saka.
Dukkan su sun bayyana cewa a wannnan harka ce suke samun kuɗin abinci da biyan buƙatun su na yau da kullum.
Discussion about this post