Gwamnatin Najeriya ta ƙwace Dala miliyan 37 daga asusun ‘yan Kirifton da ake zargi da ɗaukar nauyin zanga-zanga.
A ranar 8 ga Agusta ne EFCC ta shigar da korafi a kotu, inda ta bayyana cewa ‘kuɗaɗen kirifto’ kuɗaɗe ne na harƙalla, kuma ana ɗaukar nauyin ta’addanci da kuɗaɗen.”
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ce ta bayar da umarnin ƙwace kuɗaɗen daga cikin asusun su.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan hukunci a ranar 9 ga Agusta, kuma PREMIUM TIMES ta samu kwafen hukuncin.
Nwete ya bada umarnin kulle asusun na su ne bayan EFCC ta nemi kotun ta yi haka.
Ba a dai yi wani ja-in-ja tsakanin kotu da lauyan EFCC ba kafin kotun ta amince ya bayar da umarnin.
Baya ga wannan asusu mai Dala miliyan 37,061,867,869.3, akwai kuma wani mai Dala 443,512.37, sai asusu mai Dala 967 da kuma mai Dala 90.
EFCC ba ta bayyana sunayen masu asusun ba, waɗanda duk ta WhatsApp aka buɗe su. Amma dai majiya ta ce su na da alaƙa da ɗaukar nauyin shirya zanga-zanga da ɗaukar nauyin ta’addanci.
Discussion about this post