Fadar Shugaban Ƙasa ta maida wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar raddi.
Raddin da aka mayar masa a ranar Talata, ya biyo bayan gargaɗin da Atikun ya yi kan yadda jami’an tsaro ke nuna ƙarfi kan masu tarzoma da masu zanga-zanga.
Mashawarcin Musamman Kan Yaɗa Labarai ga Shugaba Bola Tinubu, wato Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sun yi mamakin irin kalaman da suka riƙa fitowa daga bakin Atiku.
Ya ce ai kamata ya yi Atiku ya fara gargaɗin gungun ‘yan ta-kifen da suka riƙa kwasar kayan jama’a Kano, Kaduna, Jigawa da kuma Filato, waɗanda suka ƙwace ragamar zanga-zangar daga hannun waɗanda suka shirya ta lumana.
Ya ce jami’an tsaro sun nuna ƙwarewa wajen daƙile masu tarzoma, waɗanda suka riƙa yi masu barazana sosai.
“Muna mamakin yadda Atiku ke ta kakabin jawo aya a cikin Sashe na 40 na Kundin Dokokin Najeriya, inda Atiku ya riƙa halasta zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa tarzoma da kwasar dukiyoyin jama’a a wasu jihohi.
“A matsayin sa na mai goyon bayan tarzomar da ta janyo lalata ɗimbin dukiyoyin jama’a, Atiku ya tabbata ya so wannan shiryayyar zanga-zanga ta ɗore, duk kuwa da irin munin da ta fara yi, ta tashi daga zanga-zanga zuwa mumnunar tarzoma.”
Ya ja hankalin Atiku ya riƙa amfani da hankali ba son rai ba.
“Ya-kamata Atiku ya sa kishin ƙasa a gaba, bisa ga duk wata ɓoyayyar manufar da yake son ya cimma daga tarzomar lalata ɗimbin dukiyoyin da ta ɓarke kan titina.”
Discussion about this post