Zanga-zangar rashin amincewa da ci gaba da fama da yunwa da raɗaɗin tsadar rayuwa da ta gudana tsawon kwanaki 10 a Najeriya, ta ɗauki sabon salo, ganin yadda wasu mafusatan matasa suka riƙa filfila tutar Rasha, a Arewacin Najeriya.
Ba wannan kaɗai ne abin da ya zo da sabon salo yayin zanga-zangar ba, akwai fitowa da aka riƙa yi ƙarara ana roƙon sojoji su ƙwace mulki a Najeriya. Akwai wasu ababen dubawa idan aka zurfafa kallon lamarin, saboda yawancin masu waɗannan kiraye-kirayen yara ne ƙanana, a hotuna da bidiyo ɗin da suka riƙa yawo a soshiyal midiya.
Kasancewar yawancin su yara ne, ba su san irin munin laifin da suka aikata ba, kuma ba su san abin da ka iya biyo baya ba, dangane da wannan kamfe da suka riƙa yi. Shin ko dai akwai wani gungun mutanen da ke ɓoye, waɗanda suka riƙa zuga su ne a ɓoye?
Ko ma dai mene ne, laifin da suka aikata cin amanar ƙasa ce, kuma abu ne da ba za a iya amincewa da shi ba. Dukkan wani ɗan Najeriya mai kishi ya dace ya yi Allah-wadai da masu kiran a yi juyin mulki. A matsayin mu na ƙasa, mun sha gaganiyar fama da mulkin soja, kuma mun ga illolin sa.
Jihohin da kiraye-kirayen a yi juyin mulki ya fi tayar da cida da hazo sun haɗa da Kano, Kaduna, Katsina, Bauchi da Nasarawa.
Kamar yadda aka yi tsammani, tuni jami’an tsaro sun fara ɗaukar ƙwararan matakai, musamman idan aka yi la’akari da kamen da aka yi wa mutane da dama, ciki har da wasu ‘yan ƙasar Poland mazauna Kano.
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya gana da Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasa cikin makon jiya, inda a lokacin ganawar Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa, ya shaida masa cewa lallai tabbas masu tayar da tarzoma sun riƙa kururuwar sojoji su yi juyin mulki, kuma sun tattauna wannan batun da shi Shugaba Tinubu.
Shi ma Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar ya bayyana irin haka, lokacin da yake wa manema labarai ƙarin bayanin maƙasudin ganawar da ya yi da Jakadun ƙasashen waje da ke Najeriya da sauran manyan jami’an diflomasiyya.
Tuggar ya ce Najeriya ba za ta ƙyale duk mai hannu a nan cikin gida ko daga waje, wajen ruruta wutar fitina a ƙasar nan.
Haka su ma Shugabannin Tsaro na ƙasashen ECOWAS sun yi irin wannan taron cikin makon jiya a Abuja. Sun ce tabbas sojoji na nan bisa nuna biyayyar su 100 bisa 100 kan tsarin dimokraɗiyya.
Shi ma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi tir da masu kiraye-kirayen sojoji su yi juyin mulki, a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya. Musa kuwa ya yi cewa duk mai kiran a yi juyin mulki to ya aikata laifin cin amanar ƙasa. Haka su ma Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA).
Wannan jarida na yin kakkausan kira cewa a gaggauta binciken wannan matsala, domin a hukunta masu hannu, kuma a taka masu burki, ta yadda hukuncin zai zama darasi ga wasu nan gaba.
Discussion about this post