Halin ƙunci, raɗaɗin tsadar rayuwa da masifar tsadar kayan abinci da masarufi sun haifar da ƙorafe-ƙorafe tun daga farkon hawan mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Tura ta kai ‘yan Najeriya bango, har sun kasa haƙura, inda a ranar Alhamis suka hasala, suka fita zanga-zanga kan titina, tun daga Legas har zuwa sauran garuruwa da biranen ƙasar nan.
Wannan zanga-zanga ta game-gari wadda waɗanda suka shirya ta suka ce za ta ɗauki kwanaki 10, daga ranar 1 zuwa 10 ga Agusta, ba fa wani abu ne ya haifar da ita ba, sai yunwa, fatara, talauci da masifar tsadar kayayyakin amfani na ya U da kullum, kuma na dole a rayuwa, musamman farashin abinci da na sufuri.
Duk da cewa akwai manyan ƙungiyoyi irin su ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya, wato NANS da sauran su, waɗanda ba su shiga zanga-zangar ba, duk da haka ta zama gagarima, musamman a ranar farko.
Sai dai kuma an samu ɓarkewar tashe-tashen hankula a wasu jihohi a Arewa. Amma a kudancin Najeriya zanga-zangar an yi ta ne sesa-sesa. Amma dai an samu rasa rayukan mutane da yawan gaske, duk da dai ‘yan sanda sun ce mutum bakwai ne kaɗai suka mutu, Amnesty International ta ce 13 ne suka rasa rayukan su a faɗin ƙasar nan. Amma lamarin gaskiya adadin duk ya wuce haka.
An yi ƙone-ƙone, an saci dukiyoyin jama’a musamman a Kano da wasu garuruwan Arewa. ‘Yan Sanda sun ce sun kama mutum 681, inda a Kano kaɗai aka kama mutum 320. Wannan lamari ya haifar da kafa dokar hana fita wasu garuruwan Arewa.
Cikin ‘yan kwanaki an yi gagarimar asara. Ma’aikata sun zauna gida, haka ɗalibai da ‘yan kasuwa da direbobi. Masana sun ce a ranar farko an yi asarar za ta zarce ta Naira biliyan 100.
Maimakon Gwamnatin Tarayya ta bi a hankali wajen bai wa masu zanga-zanga damar su, sai ta shirya zanga-zangar rashin goyon bayan masu zanga-zanga a rana ɗaya, lamarin da ya haifar da hasalar jama’a a Ojota, Legas. A Kano ma an shirya irin wannan zanga-zangar ta rashin goyon bayan masu zanga-zanga, duk a rana ɗaya.
An yi zanga-zangar goyon bayan Gwamnatin Tarayya a Hedikwatar Kamfen ɗin TInubu/Shettima a Abuja, inda Ƙaramin Ministan ‘Yan Sanda, Imaam Suleiman Ibrahim ya halarta.
A Kano an shirya irin ta, bisa jagorancin ɗaya daga cikin jami’in gwamnatin tarayya, inda suka taru a ƙofar Gidan Nasarawa, gidan da tsigaggen sarkin Kano Aminu Ado ke zaune. Gidan kuma ya na kusa da Gidan Gwamnatin Kano. Kuma ya na kusa da Babbar Kotun Jihar Kano, wadda masu zanga-zanga suka farfasa, suka kwashe komai, har masallacin da ke cikin harabar sai da suka yi masa ƙarƙaf.
A Abuja ‘yan sanda sun wuce-gona-da-iri, kamar yadda suka yi a wasu garuruwa. Sun bugi wakilin PREMIUM TIMES, Yakubu Mohammed da gindin bindiga, duk kuwa da cewa ya nuna masu katin shaidar shi ɗan jarida ne.
Ita kuwa Gwamnatin Tarayya sai ta yi baki-biyu. A ɗaya ɓangare ta amince a yi zanga-zanga, a gefe ɗaya kuma wasu jiga-jigan ta sun riƙa garzayawa kotu neman hana zanga-zanga.
PREMIUM TIMES ta yi tir da asarar dukiyoyin da aka yi. Kuma bai kamata a lamarin ya ci gaba a haka ba. Babban abin takaici shi ne asarar rayukan da aka yi, wanda jami’an tsaro suka yi amfani da ƙarfin makamai. Wannan mun ce tabbas babban laifi ne wanda gwamnati ba za ta iya kare kan ta ba. An harbi ɗan jarida a Legas. An ratattaka wa motar wakilin PREMIUM TIMES harsasai.
Akwai buƙatar mutanen da suka san abin da suke yi kuma suka iya mulki da hulɗa da jama’a a cikin gwamnati su fitar da ƙasar nan cikin jula-jular da ake ciki.
Gaskiyar magana Tinubu ya janyo wannan batarnaƙa yayin da ya cire tallafin fetur, kuma ya saki Naira a kasuwar canji domin ta samar wa kan ta darajar da ba ta iya samar wa kan ta, sai ma lalacewar da ta ƙara yi.
Ƙarin albashin da ya yi ba zai yi wani tasiri ba idan aka yi la’akari da yadda malejin tsadar rayuwa da tsadar farashin kayan abinci ya cilla sama. A irin wannan lamari babu abin da Naira 70,000 za ta iya yi. Kuɗin da daidai suke da Dala 44 duk wata kenan.
Zanga-zangar dai ta wuce batun yunwa kaɗai. Domin an riƙa neman a dawo da tallafin fetur, a saidaita gwamnati, a daina satar kuɗaɗen gwamnati, a ƙwato biliyoyin da ɓarayin gwamnati suka sace, a gyara tsarin zaɓe da sauran su. Akwai masu so a rage yawan ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati.
Ya kamata Tinubu ya ɗauki kukan ‘yan Najeriya da muhimmanci, ya tashi ya gyara gagarimar matsalar da ke cikin Ƙaramar tsarin tafiyar gwamnatin sa. Amma watsa wa talakawa wata ‘yar shinkafa da gero, ana maida su kamar kaji, ba fa zai magance komai ba. Yanzu ya kamata ya tashi tsaye, tun kafin lokaci ya ƙure masa.
Discussion about this post