Hukumar Bayar da Lamuni ga Ɗaliban Gaba da Sakandare ta Ƙasa (NELFUND), ta bayyana cewa a cikin watan Yuli ta raba wa ɗalibai 20,371 Naira 20,000 kowanen su domin ɗawainiyar karatun su a faɗin ƙasar nan.
NELFUND ta ce an raba kuɗaɗen ga ɗaliban makarantu shida, waɗanda suka haɗa Jami’ar Bayero ta Kano, Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, Jami’ar Ilorin, Jami’ar Benin, Jami’ar Ibadan da kuma Jami’ar Maiduguri.
Cikin wata sanarwar da Daraktan Kuɗaɗe cna NELFUND, Ibom Uche ya sa wa hannu, ya ce sun fara samun kuɗaɗen daga watan Yuli, kuma hukumar na aiki haiƙan domin tabbatar da cewa wasu makarantu aƙalla 55 sun karɓi na su nan ba daɗewa ba, cikin makonni biyu masu zuwa.
Ya ce za su tabbatar duk ɗalibin da ya cancanci karɓar lamunin ya samu.
NELFUND ta ce kuɗaɗen da ta raba ga ɗaliban na jami’o’i shida Naira biliyan 2 ne. Yayin da jami’ar Bayero ta samu Naira miliyan 853, Jami’ar Maiduguri ta samu Naira miliyan 589, sai FUDMA Naira miliyan 304, wato makarantar da ke Dutsinma ta Jihar Katsina.
Jami’ar Ibadan Naira miliyan 201, Jami’ar Ilorin Naira miliyan 52, sai Jami’ar Benin Naira miliyan 24.
Discussion about this post