Mako ɗaya bayan masu tayar da tarzoma sun fake cikin ‘yan zanga-zanga sun kwashi dukiyoyin gwamnati da na jama’a a Jihar Kano, waɗanda suka tafka asara sun fara fitowa su na magana.
Mariya, mahaifiyar ƙasaitaccen attajiri, Aliko Ɗangote, ta na ɗaya daga cikin waɗanda suka tafka wannan asara.
A Kano an lalata wurare da dama tare da kwashe abinci da kayayyaki na biliyoyin nairori.
Mazauna unguwar Sarari a Ƙaramar Hukumar Dala, inda mahaifiyar Ɗangote ke ajiye kayan abincin tallafin da take rabawa a kowace rana, sun shaida wa PREMIUM TIMES yadda ‘yan ‘kwasar ganima’, kamar yadda suke kiran kan su, suka yi wa Mariya asara ta sama da Naira biliyan 5.
Kanzillahi Nasiru ya ce masu kwasar kayan su na ɗauke da muggan makamai, sun kewaye wurin suka dumfari gangamemen rumbun ajiye kayayyakin. Sun kori masu gadi, suka lalata kyamarar CCTV kafin su fara jidar kayan.
“Da ido na na ga yadda suka lalata CCTV kyamara, wadda aka kafa tsallaken rumbun ajiye kayayyakin. Sun samu ƙofar suto ɗin a buɗe, kawai suka afka, su ka ci gaba da jidar buhunan suga da filawa. Daga nan kuma waɗanda suka isa daga baya suka je su na jidar buhunan gero da na masara.” Inji Nasiru.
“Bayan sun lalata kyamarar, sun fara kwasar kayan, sai yaya na ya ce na koma na shiga cikin gida, na daina tsayawa ina kallon su. To daga nan ina cikin gida na fara jin ƙarar bindiga, tiyagas na tashi, wanda ‘yan sanda suka riƙa harbawa.
“To daga nan ne ‘yan sanda suka tarwatsa masu jidar kayan.”
Ya ce a lokacin babu matasa a cikin unguwar waɗanda za su iya hana masu kwasar kayan, saboda sun tafi wurin zanga-zangar da ba ta kwasar ganima ba.
Shi kuwa Abdulsalam Muhammad cewa ya yi mahaifiyar sa ce ta gargaɗe shi, ta ce kada ya kuskura ya fita daga gida.
“Can sai na riƙa jin hayaniya, ina fita sai na ga gungun jama’a na jimamin wasu ‘yan kwasar kaya daga wata unguwa sun shigo unguwar mu sun kwashe kayan abincin tallafin da Hajiya Mariya ke rabawa ga marasa galihu.”
Akwai kuma masu kantina irin su Barakat, Sahad da Rufaidah Yoghurt da su ma suka tafka asara.
Jami’in Barakat Stores, Muhammad Sani ya ƙiyasta cewa sun yi asara za ta kai ta Naira biliyan 5. Ya ce ma’aikata kamar 300 ne suka rasa aiki bayan kwashe masu kayayyaki.
“Abin da muka yi asara zai kai Naira biliyan 5. Akwai kwantinoni 2 daga Chana maƙare da kaya, akwai wasu 2 da rabi maƙare da kaya daga Turkiyya, kwanan nan aka shigo da su, amma duk sun kwashe su.
“Sun ɗauki man girki guda 1000, wanda ko biya ba mu kai ga yi ba. Bai fi kwanaki uku da kawowa ba suka kwashe su. Sun kwashi kaya na lodin mota 30 da aka kawo daga Legas. Sun lalata mana motar raba kayayyaki wadda kwanan nan muka saye ta Naira miliyan 15.” Inji Sani.
Sauran wuraren da aka kwashi kaya sun haɗa da Gandun Albasa a Kano, a makarantar Alqur’ani ta Shehu Sagagi, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Kano. Makarantar ta yara ce marasa galihu da kuma marayu.
Haka kuma a Babbar Kotun Kano an kwashi kayayyaki, an lalata kayan da ake kafa hujjar shaida da su daga waɗanda ake tuhuma da sauran kayayyaki.
Discussion about this post